Jummaʼa 22 Mayu 2026 - 13:58
Yadda Za a Kasance Tare da Ahlul‑Baiti (AS) a Duniya da Lahira

Hauza/ Ayatullah Jawadi Amuli ya ce: "Ba zai yiwu mutum ya kai matsayin Imami ba, amma yana yiwuwa ya kai matsayin dalibansu. Su ma mutane ne kamar kowa da suka kai wannan matsayi.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Ayatullah Jawadi Amoli a cikin wani bayani game da “Imamai tsarkaka (AS) da kuma wadanda suka tarbiyyantar a makarantar su” ya bayyana cewa: "Kai wa matsayin Imami ba zai yiwu ba, amma kai wa matsayin dalibansu yana yiwuwa. Su ma mutane ne kamar kowa da suka kai wannan matsayi. Ba Imamai ba ne, kuma ba ‘ya’yan Imamai ba ne; mutane ne na yau da kullum da ta hanyar kokari da neman ilimi suka zama daga cikin waliyyan Allah. Idan da wannan hanya ba za ta yiwu ba, da ba za a yi wannan yawan kwadaitarwa da umarni domin bin ta ba.

Imam Ja’afar al‑Sadiƙ (AS) ya ce:  

«نعم الشفیع أنا وأبی لِحمران بن أعین یوم القیامة نأخذ بیده ولا نزایله حتی ندخل الجنّة جمیعاً»

“Ni da mahaifina mu ne zamu kasance masu yin ceto ga Humran bin A‘ayan a ranar kiyama; za mu rike hannunsa kuma ba za mu sake shi ba har sai mun shiga aljanna tare da shi.”

Humran bin A‘ayan matashi ne ma'amuli wanda daga baya ya zama malami kuma ya kai wannan matsayi. Saboda haka ba daidai ba ne mutum ya ce kai wa matsayin waliyyan Allah abu ne mai matukar wahala. A ranar kiyama za a gane cewa hanyar a bude take, amma mu ne ba mu bi ta ba.

(Madogara: Bihar al‑Anwar, juzu’i na 47, shafi na 351)  

Hikmat al‑Ibadat, shafi na 267.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha